Manchester United ta je ta doke West Ham United da ci 2-1 a wasan mako na biyar a gasar Premier League ranar Lahadi.
Said Benrahma ne ya fara ci wa West Ham kwallo a minti na 30 da fara take tamaula, sai dai minti biyar tsakani Cristiano Ronaldo ya farke.
Kwallon da Ronaldo ya ci West Ham ya zama fili na 66 da ya zura kwallo a raga a tsakanin manyan gasar Turai biyar, tun bayan da ya fara buga wa Manchester United tamaula a 2003/04, yana kan gaba da Zlatan Ibrahimovic mai 64.
Haka kuma kwallo na hudu da ya ci wa United a wasa uku, bayan da ya koma Old Trafford a bana daga Juventus, har da wadda ya zura a biyu da ya zura a ragar Newcastle United a Premier League da dayan da ya ci Young Boys a gasar Champions League ranat Talata.
A minti na 89 Jesse Lingard ya ci wa Manchester United na biyu, watakila hakan ya wanke zuciyar magoya bayan United, bayan da shine ya yi kuskuren bayar da kwallo Young Boys ta ci United ta biyu ranar Talata a gasar Zakarun Turai.
Lingard ya zama na 47 da ya zura kwallo a ragar West Ham, kuma ya ci mata a lokacin da ya buga mata wasannin aro a bara, kuma West Ham ce kan gaba da take da yawan ‘yan wasan da suke buga mata wasa su ci mata kwallaye, idan sun barta su kuma zura mata kwallo a ragarta.
A cikin karin lokaci ne West Ham ta samu bugun daga kai sai mai tsaron raga, inda Mark Noble ya buga, sai dai golan United, David de Gea ya tare ta kasa shiga raga, kuma karon farko da ya buge fenariti tun cikin watan Afirilun 2016 a United da kuma tawagar Sifaniya.
Tun kafin ranar ta Lahadi an zura kwallo 40 a ragar De Gea a jere a bugun fenari da aka buga masa a kungiya da a Sifaniya.
Source: www.bbc.com